Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram ta kashe mutane 40 a kwanan nan


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

A Najeriya kalla mutane 40 ne aka kashe a harin baya-bayan nan da kungiyar ta'adda ta kai a arewacin kasar.

Shedun gani da ido da kuma majiyar jami'an tsaro sun ce, wannan harin ya faru ne a wasu kauyuka da ke makwabtaka da juna a jihar Borno a ranakun Litinin da Talata.

Mazauna wadannan kauyukan da suka samu damar arcewa sun shaidawa Muryar Amurka cewa, maharan sun shigo musu ne akan babura da motocin bas, suka shiga kona gidaje tare da kashe mutane ba kakkautawa da kwace kayayyakin abinci daga hannun jama'a

Ko ranar Littinin din nan data gabata sai da wata 'yar kunar bakin wake ta tada bam a kasuwar kifi dake kusa da wani masallaci a garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Boko Haram ta kara kaimi wajen kai hare-haren tun bayan da sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci babbar rundunar sojin kasar da ta matsar da shelkwatarta ta daga Abuja zuwa Maiduguri don yakarsu.

XS
SM
MD
LG