Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Tayi Raga-raga da Baga


Yadda garin Baga ya zama bayan harin Boko Haram

Kungiyar kare hakkin Bil 'Adama ta bada cikakken bayanin irin barnar da kungiyar Boko Haram tayi a Baga

Kungiyar nan dake rajin kare hakkin Bil'Adama Amnesty International ta fidda hotunan da aka dauka da tauraron dan'adam ko satellite da turanci, da suka nuna irin barnar da mayakan sakai na Boko Haram suka yi a arewa maso gabashin Najeriya.

Hotunan da kungiyar ta nuna kamin akai harin da kuma bayan an kai harin akan Baga da kuma Doron Baga, sun nuna gine gine 3,700 da aka kona su kurmus bada jumawa ba, bayan da kungiyar ta kama Baga ranar 3 ga watan nan na Janairu.

Galibin gidajen da mayakan suka lalata a Doron Baga ne, inda wani mai nazari na kungiyar ta Amnesty Daniel Eyre yace, "kusan an share garin baki daya, daga doron kasa, cikin kwanaki hudu kacal".

Kungiyar kare hakkin Bil'Adaman tace, a hirarraki da tayi da shaidun gani da ido, sun ce mayakan sakan sun harbe daruruwan fararen hula ciki har da yara kanana da kuma wata mace da take nakuda.

Rundunar sojojin Najeriya tace mutane dari da hamsin ne aka kashe a Baga, amma jami'an yankin sun ce ta yiwu wadanda aka kashen sa haura dubu daya.

Kungiyar Amnesty ta fada jiya Laraba cewa, bisa laka'ari da bincike da ta gudanar ya nuna cewa Boko Haram ta kai hari kan Baga ne domin garin ya kasance sansanin 'yan kato da gora, ko civilian JTF, wadanda suke taimakawa sojoji.

Tunda farko a wunin jiya, rundunar sojojin Najeriya a shafinta na dandalin Twitter, tace ta wargaza wani yunkurin kai hari kan garin Biu da 'yan binidgar suka so suyi. Rundunar tace sojoji suna farautar 'yan binidgar bayan da suka kama biyar daga cikinsu, da makamai na harbo jiragen sama biyu.

XS
SM
MD
LG