Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bola Ahmed Tinubu Ya Sha Rantsuwar Kama Aiki


An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya
An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya

An rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Kasar Najeriya.

Babban mai shari’a na Najeriya Kayode Ariwoola ne ya rantsar da Tinubu da misalin karfe 10:37 na safe agogon kasar, a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Ya hau dandamalin rantsuwar tare da matarsa, Sanata Oluremi Tinubu, da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Buhari, inda suka tsaya a bayan Tinubu yayin da ya ke shan rantsuwar kama aiki.

An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya
An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya

Tun da farko dai, Kashim Shettima, ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa da misalin karfe 10:28 na safe a gogon kasar.

Bola Ahmed Tinubu da ake wa kirari da Jagaba Borgu, ya kasance tsohon gwamnan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya na yankin kabilar Yarbawa.

An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:26 0:00

Tinubu kamar yadda aka fi saninsa, ya fara makarantar sakandare a Ibadan, kafin ya karashe a Kwalejin Richard Daley da ke birnin Illinois a jihar Chicago a kasar Amurka.

Bayan ya kammala sakandare ya kuma halarci Jami'ár jihar Chicago inda ya karanci Degree a fannin Akanta tare da kammalawa a shekarar 1979.

Kafin ya dawo Najeriya, ya yi aiki a kasar ta Amurka a kamfanonin Akanta daban-daban.

An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya
An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya

Bayan komowarsa gida ne kuma ya shiga harkokin siyasa, inda ya shiga kungiyar People Front ta marigayi Janar Shehu Musa Yaradua, kafin daga bisani su rikide zuwa jamiyar SDP, inda kuma a nan ne ya tsaya takarar Sanata mai wakiltar Legas ta Yamma, tare kuma da samun nasara.

Sabon Shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Sabon Shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Bayan da sojoji suka soke zaben 12 ga watan Yuni da aka fi sani da zaben Abiola, Tinubu da wasu ‘yan siyasa, musanman daga kudancin kasar, sun tafi gudun hijirah tare kuma da kafa wata kungiya ta ‘yan adawa da mulkin soji mai suna NADECO.

A yayin da sojoji suka kada gangar siyasa a 1998, Bola Tinubu ya dawo gida, ya tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyar AD ko Alliance for Democracy, inda ya mulki jihar Legas tsawon shekaru takwas.

A wannan lokaci ne dai Tinubu ya kafa abin da ake ganin jam’iyar siyasa da magoya baya da dama da suka zame masa jari a tafiyar siyasarsa ta neman shugabancin Najeriya a wannan lokaci.

Bola Tinubu ya kasance ginshiki wajen ci gaban jihar Legas ta fuskar tattalin arziki, siyasa da kuma abin koyi ga sauran jihohin kasar wajen dogaro da kai da samun kudaden shiga.

Farin jininsa ya karu ne a siyasar Najeriya wajen sunan da ya yi wajen mara wa ‘yan Arewa baya a siyasa, tun daga marigayi Janar Shehu Musa ‘Yaradua, zuwa Atiku Abubakar da Nuhu Ribado sai kuma tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a karkashin jamiyar APC mai Mulki a yanzu.

XS
SM
MD
LG