Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom Ya Fashe A Gaban Ofishin Jakadancin Amurka A China


Wani mutum ya ji rauni lokacin da wani bom da yake dauke da shi da aka kera a cikin gida ya fashe a gaban ofishin jakadancin Amurka dake birnin Beijing yau Alhamis.

Yan sandan Beijing sun gano wani dan shekaru 26 dan asalin yankin Mangolia dake China a matsayin dan kunan bakin waken.

Harin ya auku ne kusa da gurin da mutane ke layin shiga ofishin jakadancin Amurka neman visa.

Hotunan da aka watsa a yanar gizo ya nuna yadda hayaki ya mamaye samaniya a wajen ofishin jakadancin a birnin China. Ofishin jakadancin Amurka a China na wani bangaren dake makwabta da ofisoshin jakadacin wadansu kasashe, kamar India da Israila.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG