Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

Bom Ya Tashi Cikin Ofishin Kamfe A Kudancin Afghanistan


Wani dan kunar bakin wake ya abkawa wani dan takarar majalisar dokoki a yankin kudancin Afghanistan, wanda yayi sanadin mutuwar magoya bayan shi mutun 9, kwana daya bayan da kungiyar ‘yan ta’adda ta Taliban, ta ce za ta hana gudanar da zaben da hare-hare.

Hukumomin sun ce dan-kunar bakin waken ya abka ne cikin ofishin kamfe na lardin Lashkargah, babban birnin lardin Helmand. Mai magana da yawun ‘yan-sanda Abdul Salam Afghan, ya shaida wa Muryar Amurka cewar, bom din ya raunata mutane 15, ya kuma bayyana sunan dan takarar da aka kashe da cewa Saleh Mohammad da ke neman kujerar majalisar dokokin jihar.

Shaidun gani da ido sun ce, su na kyautata zaton jimillar mutanen da za su mutu daga harin za ta karu da yake lokacin da bon din ya tashi akwai mutane da dama a cikin ofishin.

A jiya Litinin ne kungiyar Taliban ta ce ta umurci dakarunta da su shiga kai hare-hare akan rumfunan zabe da ma'aikatan tsaro don hargitsa zaben.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG