Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Bukaci Wasu Sanatoci Biyu Su Mika Kansu


Wani mutum na wucewa ta kusa da motar 'yan sanda

Hedkwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya ta umarci wasu ‘yan Majalisar Dattawan kasar biyu da su kai kansu hedkwatar ‘yan sanda a babban birnin tarayya.

Wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan Najeriyar Mr. Moshood Jimoh, ya aikowa Muryar Amurka, ya ce ana gayyatar Sanata Dino melaye da Ben Murray Bruce da su kai kansu hedkwatar ‘yan sanda a Abuja don gudanar da bincike akansu.

Tun karshen makon daya gabata ne wasu jiga-jigan ‘yan PDP suka gudanar da zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben gwamna a jihar Osun, inda suka ce an tafka magudi.

Baya ga sanatocin biyu, cikin wadanda suka gudanar da zanga zangar akwai shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki da gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal da sauran wasu hamshakai.

Amma rundunar ‘yan sandan ta ce Sanatocin biyu Watkins Dino Melaye da Ben Bruce, yanzu su take fara tuhuma bisa zargin tayar da hankali da kuma rufe hanyar Shehu Shagari, al'amarin da jami’an tsaron ke cewa ya jefa Jama’a cikin takura.

Rundunar ‘yan sandan kazalika kuma na zargin sanatocin biyu da yunkurin hana ‘yan sanda yin aikin su da kuma barnata dukiyoyin jama'a da ma na ‘yan sandan.

Yanzu haka dai ‘yan sandan sunce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG