Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BORNO: Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane Biyar a Mandarari


2Lt. Adeosun kwamandan dakarun sojin dake yaki da 'yan Boko Haram masu kai harin kunar bakin wake

Wasu mata biyu sun kai harin kunar bakin wake a Mandarari dake cikin karamar hukumar Konduga wanda ya hallaka mutane biyar tare da raunata wasu guda shida a ranar Alhamis.

A sanarwar da mataimakin jami'in rundunar 'yansandan dake jihar Borno mai hulda da jama'a Murtala Ibrahim ya aikewa manema labarai ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma yace tuni suka kwashe wadanda harin ya rutsa dasu.

Ko a jiyan ma rundunar 'yansandan ta tabbatar da tashin wani bam din da tace ya auku a daren Laraba ya kuma rutsa da mata uku 'yan kunar bakin waken.Matan sun yi kokarin afkawa cikin birnin Maiduguri ne amma jami'an tsaro suka taka masu birki ta hanyar bindigesu kafin bamabaman su tarwatse.

Hare-haren kunar bakin wake sun zama tamkar ruwan dare gama gari a Maiduguri da kewaye duk da matakan da jami'an soji suke dauka..

Ga rahoton Haruna Dauda da karinbayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Facebook Forum

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG