Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Borno: Yadda Aka Kai Hari a Garin Auno


Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum a ziyarar gane wa ido.
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum a ziyarar gane wa ido.

Gwamnan Jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zullum, ya ce duk da cewa jami'an sojin Najeriyan sun samu rahotannin yiwuwar a kai hari garin Auno ko kuma Jagana tun da misalin karfe uku na ranar Lahadi, babu wani mataki da jami’an tsaro suka dauka na kare aukuwar wannan harin.

Da daren ranar Lahadi ne wasu mahara da ake zaton ‘ya’yan kungiyar Boko Haram ne, suka far ma wannan gari na Auno, wanda ke da tazarar kilomita 121 da babban birnin Maiduguri. Maharan sun yi ta banka wa motoci da ma gidajen mutane wuta.

Tun da sanyin safiyar ranar Litinin ne gwamnan ya ziyarci wannan garin domin jajantawa mazauna garin.

A jawabinsa ga jami’an sojjin Najeriya, gwamnan ya ce daga ranar da akak rantsar da shi izuwa wannan lokaci, anfar ma wannan gari na Auno akalla sau shiddai.

Gwamnan ya bayyana takaicinsa, a game da cewa, akwai wasu motoci uku da maharan suka cika da mata da yara kuma suka tafi da su.

Kwamandan rundunar sojojin Najeriya na operation lafiya Dole manjo janar Olushegun Adeniyi ya ce, zasu kara kaimi kan kokarin da sukeyi don ganin cewa sun kawo karshen irin wadannan matsaloli.

Domin cikakken bayani a saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG