Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BORNO: ‘Yan Boko Haram Sun Kai Hari ‘Kauyen Mussa Suka Saci Abinci


Boko Haram

Rahotanni da ke fitowa da ga karamar hukumar Askira/Uba dake jihar Borno, na nuni da cewa wasu mahara da ke kyautata tsammanin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a daren Asabar kan wani ‘kauye da Mussa, inda su kayi ta musayar wuta da mutanen ‘kauyen.

Mazauna ‘kauyen Mussa dai sun ce maharan sun bude musu wuta, duk da cewa basu kashe kowaba sai dai sun raunata wasu mutane takwas sannan kuma suka kwashe musu kayayyakin abinci.

Lokuta da yawa dai irin wannan maharan kan kai hari kan wannan ‘kauye da ake kira Musa dake karamar hukumar Askira/Uba, wanda wasu lokuta akan ce sun kwashewa mutanen ‘kauyen dabbobi, sai gashi wannna karon sun kwashe abincin da ke ‘kauyen baki ‘daya, lokacin da mazauna kauyen suka fice don gudun tsira da ransu.

Da suke tabbatar da faruwar wannan lamari wasu mazauna kauyen sun shaidawa wakilin Muryar Amurka cewa, ‘yan Boko Haram ne suka kai musu hari cikin dare, inda suka raunata mutane takwas suka kuma kwashe kayayyakin abinci.

A ranar Asabar dinne wasu ‘yan gudun hijira suka rasa rayukansu da aka ce sun fito ne daga garin Bama, wadanda kuma ke zaune a sansanin ‘yan gudun Hijira da ke Dalori, sakamako yankan rago da aka ce wasu ‘yan Boko Haram sun yi musu, lokacin da suka fita farauta zuwa bayan Maiduguri.

Domin karin bayani ga rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG