Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Barno Zata Kai Karar Likitoci Data Horas, Amma Suka Ki Yiwa Jihar Aiki.


Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo

Gwamna Kashim Shettima wanda yayi wannan barazanar yace jihar zata wallafa sunayen irin wadannan likitoci a jaridu.

Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima yayi barazanar zai kai karar Likitoci da jihar ta dauki nauyin horas da su, amma bayan bayan sun kammala kwas sai suka ki yiwa jihar aiki.

Gwamnan yayi wannan barazanar ce lokacinda ya karbi bakuncin tsoffin daliban makarantar yerwa wadanda suka kai kai masa chaffa a ofishinsa.

Gwamnan yace yanzu haka sun kammala yiwa asibitin Beni-Sheikh garambawul, suna neman likita wanda za'a bashi gida da mota kyauta, amma sun kasa samun Babarbare, dan arewacin jihar wanda zai je yankin domin yayi aiki.

Gwamna Shettima yace lokaci ya wuce da 'yan yankin zasu rinka gudu daga bautawa jama'ar da suka dauki nauyin karatunsu.

Gwamnan yace jin kunya mara kunya tsoro ne, saboda a shirye gwamnatinsa take ta kunyata irin wadannan 'yan jihar wadanda suka yi alkwari zasu yiwa Barno aiki, amma bayan da suka kammala horo, suka gudu daga jihar ko suka fada wasu masana'antu inda akwai maiko.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG