Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bouteflika Ya Yi Biris Da Masu Bore, Ya Nada Shugaban Yakin Neman Zabensa


Shugaban Algeria, Abdelaziz Bouteflika a shekarar 2017
Shugaban Algeria, Abdelaziz Bouteflika a shekarar 2017

Shugaba Bouteflika ya zabi ministan sufurinsa Abdelghani Zaalena wanda zai maye gurbin tsohon firai minista Abdelmalek Sellal a matsayin Darektan gangamin yakin neman zabensa a zaben da ke tafe.

Kwana guda bayan da dubban ‘yan kasar Algeria suka yi zanga zangar adawa da yunkurin da shugaba Abdelaziz Bouteflika yake yi na neman wa’adi na biyar, shugaban ya nada sabon shugaban gangamin yakin neman zabensa.

Shugaba Bouteflika ya zabi ministan sufurinsa Abdelghani Zaalena wanda zai maye gurbin tsohon firai minista Abdelmalek Sellal a matsayin Darektan gangamin yakin neman zabensa a zaben da ke tafe, kamar yadda wata sanarwa ta nuna, wacce kamfanin dillancin labaran kasar ta Algeria wato APS ya wallafa a jiya Asabar.

A ranar 18 ga watan Afrilu kasar ta Algeria za ta gudanar da zaben shugaban kasa.

A dai shekarar 2013, shugaba Bouteflika mai shekaru 82, ya samu matsalar shanyewar barin jikinsa, lamarin da ya sa ba kasafai ake ganinsa a baina jama’a ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG