Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ba Zai Karbi Masu Gaisuwar Sallah Ba - Fadar Gwamnati


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi sallar Idin layya a gida tare da iyalansa kamar yadda ya yi a lokacin karamar sallah, a wani mataki na takaita yaduwar cutar Covid-19, a cewar wata sanarwa da ta fito daga fadarsa.

Babban mai baiwa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da fadar ta fitar a yau Laraba.

Sanarwar ta kuma ce Shugaban ba zai karbi baki a bana ba wadanda suka saba zuwa domin kawo masa gaisuwar sallah.

Shehu ya ce an dauki wannan matakin ne sakamakon shawarwari da aka samu daga majalisar koli ta adinin musulunci domin takaita cutar ta Coronavirus.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma jaddada matakan da majalisar ta ba da shawarar a bi na kaucewa tarurrukan da mutane da dama za su kasance a wuri daya.

A bikin karamar sallah da aka yi a wannan shekarar, shugaban ya yi sallar Idinsa a gida tare da iyalansa maimakon zuwa masallaci yadda ya saba yi a kowace shekara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG