Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Na Jajen Mutuwar Mace Ta Farko Da Ta Fara Tuka Helikwaftan Yaki a Najeriya


Tolulope Arotile
Tolulope Arotile

Shugaba Buhari na Najeriya ya jajantawa 'yan uwan mace ta farko da ta fara tuka jirgin helikwaftan yaki a Najeriya, wacce ta rasa ranta sanadiyyar wani hadarin mota.

Tolulope Arotile ta rasu ne a jihar Kaduna a ranar Talata bayan da ta samu wasu munanan raunuka a kanta.

Buhari ya jaddada kwazon Arotile wajen yaki a fagen daga domin kare Najeriya daga 'yan bindiga da 'yan ta'adda kuma ya ce ba za a taba mantawa da kokarinta ba.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar gwamnati mai dauke da sa hannun mai baiwa shugaban shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina.

'Yar shekaru 23 din wacce 'yar asalin jihar Kogi ce ta girma a Kaduna inda ta nuna sha'awar aikin soji tun tana yarinya.

Tolulope Arotile
Tolulope Arotile

Mutuwar Arotile ta girgiza 'yan Najeriya da dama, ciki har da babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadiq Abubakar wanda ya wallafa irin kokarin marigayiyar a shafinsa na Twitter.

"Tana da fasaha sosai, duk inda ta je za ta nuna irin baiwar da ta ke da ita. Ta taka muhimmiyar rawa a kokarin dakile 'yan ta'adda a jihar Neja. Mutuwarta babban rashi ne gare mu," a cewar Air Marshall Abubakar.

Sakon Air Marshall Sadiq kan mutuwar Tolulope
Sakon Air Marshall Sadiq kan mutuwar Tolulope

Gwamnan Kogi Yahaya Bello shima ya nuna yadda mutuwar ta taba shi a cikin wani sakon da ya fitar.

Kafin mutuwarta, Arotile ta zama jaruma wacce matasa mata da dama ke kwaikwayon zama kamarta kasancewar tana aiki a faggen da ba a saba ganin mata ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG