Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Na Ziyarar Aiki a Bauchi


Buhari a Bauchi
Buhari a Bauchi

Shugaba Buhari na ziyarar wuni guda a Jihar Bauchi domin kaddamar da wasu ayyuka kamar, sabon asibitin sojojin sama, da hanyoyin da aka yi musu kwaskwarima da kuma kayyakin aikin gona.

A ziyarar, Shugaba Buhari ya bukaci ganin 'yan siyasa sun gudanar da yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali tare da jaddada anniyarsa na kame duk wanda ya saci kudaden al'umma har sai maidosu.

Sai dai jam'iyyar adawa ta PDP ta soki gwamnatin APC a jihar Bauchi da cewa babu wani abu mai muhimmanci da ta yi illa yaudarar jama'a da jihar.

"Babu abun da aka yi a jihar Bauchi sai dai abubuwan da aka tarad muhimmai wanda akayi yi su lokacin mulkin sojoji, ko na zamanin Gwamna Ahmed Mua'zu da na Yuguda, su ne aka samu ake musu fenti, su din ma wasu ma an lalata saboda ha'inci." inji kakakin jam'iyyar PDP reshen Bauchi, Alhaji Yaya Inuwa Zainabari.

Saurari cikakken rohoton Abdulwahab Muhammad

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG