Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Bukaci Manyan Hafsoshin Soji Su Samar Da Tsaro Kafin Faduwar Damuna


Manyan Hafsoshin sojin Najeriya (Hoto: Twitter Sojojin sama na Najeriya).
Manyan Hafsoshin sojin Najeriya (Hoto: Twitter Sojojin sama na Najeriya).

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fadawa manyan hafsoshin sojin kasar cewa ‘yan makonnin suke da shi domin maido da cikakken tsaro a kasar.

Buhari​ ya kalubalanci manyan sojojin ne yayin wani biki da aka yi a fadar gwammnatin kasar inda aka musu ado da aninai daban-daban a ranar Juma’a.

Shugaban ya kara da cewa, yana fatan za su cimma wannan buri na tabbatar da tsaro nan da zuwa faduwar damuna domin manoma su koma gwanakinsu a sassan kasar.

“Makonnin kadan suka rage muku ku aiwatar da hakan, saboda nan da zuwa faduwar damuna, muna fatan mutane za su samu kwarin gwiwar zuwa gonakinsu don su yin noma. Saboda kada mu yi sakaci a ki zuwa gonaki, gudun kada a gaza samar da wadataccen abinci da kasa za ta ci.” Buhari ya ce.

Karin bayani akan: Laftanar Janar Tukur Buratai, Buhari​, Nigeria, da Najeriya.

Ya kuma tunashe su da su kalli wannan nadi da aka musu a matsayin alama da ke nuna ana da kwarin gwiwa akansu.

Buhari yana sakawa shugaban hafsan sojin sama aninai (Hoto: Twitter Nigerian Air Force)
Buhari yana sakawa shugaban hafsan sojin sama aninai (Hoto: Twitter Nigerian Air Force)

A ranar 27 ga watan Janairu Buhari ya amince da murabus din manyan hafsoshin sojin da suka hada da babban hafsan tsaro na kasa, Janar Abayomi Olonisakin da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da kuma babban hafsan sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar.

Sabbin manyan hafsoshin sojin da suka gaje su sun hada da Manjo Janar Leo Irabor a matsayin babban hafsan tsaro na kasa, da Manjo Janar I. Attahiru a matsayin babban hafsan sojin kasa.

Sai kuma Rear Admiral A.Z Gambo a matsayin babban hafsan sojin ruwa, da kuma Air-Vice Marshal I.O Amao a matsayin babban hafsan sojin sama.

Buhari yana sakawa shugaban sojin kasa hula (Hoto: Twitter Nigerian Army)
Buhari yana sakawa shugaban sojin kasa hula (Hoto: Twitter Nigerian Army)

In za a tuna dai, mutane da dama a Najeriyar sun yi ta yin kira ga shugaban kasar da ya canja manyan hafsoshin tsaron, ganin yadda matsalar tsaro a kasar ke ci gaba da tabarbarewa.

Sai dai a baya shugaba Buhari bai saurari kiraye-kirayen sauke manyan hafsoshin ba, abin da ya sa masu sharhi kan sha’anin tsaro ke nuna shakku a ikirarin gwamnatin kasar na yaki da ‘yan bindiga musanman mayakan Boko Haram.

Abin jira a gani yanzu shi ne, ko wadannan sabbin manyan hafsoshin soji da aka nada za su kawo babban canji da mutane suka dade su na jira na kawo karshen matsalolin tsaro da kasar ke fama su.

XS
SM
MD
LG