Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Ce A Hukunta Duk Wanda Ke Da Hannu A Hare-haren Benue


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito hukumomin tsaro a yankin da lamarin ya faru suna cewa, akalla mutum 74 aka kashe cikin makon da ya gabata a wasu hare-hare biyu da ‘yan bindiga suka kai a jihar ta Benue.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a jihar Benue, inda aka kashe gomman mutane a yankin Umogidi da ke karamar hukumar Otukpo.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, Buhari ya yi kira da a dauki duk matakan da suka dace wajen ganin an dakatar da rikicin tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi a fadan.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito hukumomin tsaro a yankin da lamarin ya faru suna cewa, akalla mutum 74 aka kashe cikin makon da ya gabata a wasu hare-hare biyu da ‘yan bindiga suka kai a jihar.

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom

Sai dai yayin da ya kai ziyara yankunan da aka kai hare-haren a ranar Asabar, Gwamnan jihar Samuel Ortom ya ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 134 kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

Ortom ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi maza-maza ta kai wa al’umar yankin daukin gaggawa.

Tuni dai Shugaba Buhari ya umuraci hukumomin tsaro da su sauya matakan tsaro a yankunan jihar ta Benue domin kaucewa aukuwar hakan a gaba.

Rikicin ya faru ne a wani yankin da aka saba fada tsakanin makiyaya da manoma a jihar ta Benue wacce tsakiyar arewacin Najeriya.

XS
SM
MD
LG