Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Gana Da Shugabannin Jihar Benue


Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin jihar Benue a lokacin da suka gana da shugaba Buhari
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin jihar Benue a lokacin da suka gana da shugaba Buhari

A wani yunkuri na dakile yaduwar rikicin jihar Benue da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin al'umomin da ke jihar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tattauna da shugabannin al’umomin da ke jihar Benue wacce ta ke fama da rikicin manoma da makiyaya.

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a ‘yan makwannin da suka gabata a jihar ta Benue saboda hare-haren daukar fansa da aka rika samu a jihar ta Benue.

Daga cikin wadanda shugaban ya gana da su har da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya.

“Shugaba Buhari ya jajanta wa al’umomin jihar tare da nuna damuwarsa kan wannan fitina.” Inji Malam Garba Shehu a wata tattauna wa da ya yi ta wayar talho da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa.

A cewar Shehu, shugaba Buhari ya fadawa mahalarta taron cewa, “duk wani wanda aka samu da laifi wajen wannan kashe-kashe sai an tono an yi maganin shi.Hukunci kuma ba bangare guda ba, domin barnar nan duk bangarorin nan ana yi musu ita.”

Shugaba Buhari a cewar Malam Shehu ya kuma yi kira ga shugabannin da su koma su fadawa jama’arsu su kwantar da hankulansu.

Jihar Benue a ‘yan makwannin nan ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya inda bangarorin suka rika kai hare-haren daukar fansa.

Wannan lamari ya sa shugaba Buhari ya umurci babban Sifeto Janar na rundunar ‘yan sandan kasar da ya yi kaura ya koma jihar domin a dakile lamarin.

Saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Umar Faruk Musa domin jin tsokacin da shugabannin da suka halarci wannan taro suka yi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG