Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Gana Da Tambuwal Kan Matsalar Tsaro A Sokoto


Tambuwal, hagu, Buhari, dama (Facebook/Femi Adesina)

Ziyarar ta Tambuwal a fadar ta Aso Rock na da nasaba da matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa a yankin jihar ta Sokoto da makwabtanta.

Gwamnan jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya Aminu Tambuwal ya kai ziyara fadar shugaban kasa.

Ziyarar ta Tambuwal a fadar ta Aso Rock na da nasaba da matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa a yankin jihar da makwabtanta.

Tambuwal wanda dan jam'iyyar PDP mai adawa ne, ya je fadar ne ‘yan kwanaki bayan da wata tawaga da shugaba Muhammadu Buhari ya tura jihar ta Sokoto da Katsina karkashin jagorancin mai ba shugaba shawara kan sha’anin tsaro Janar Babagana Munguno, don yin jaje bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai.

Bayanai sun yi nuni da cewa Aminu Tambuwal ya je ganin shugaba Buhari ne don yi masa bayani kan halin da ake ciki a jiharsa.

Buhari, hagu, Tambuwal, dama (Facebook/Femi Adesina)
Buhari, hagu, Tambuwal, dama (Facebook/Femi Adesina)

A ‘yan kwanakin da suka gabata ne ‘yan bindiga suka kona wasu matafiya 23 da ke kan hanyarsu ta zuwa kudancin Najeriya a yankin jihar ta Sokoto, lamarin da ya janyo kakkausar suka da zanga zanga a sassan arewacin Najeriya.

Jihar Katsina wacce shugaban kasa ya fito, ita ma ta sha fama da hare-hare iri-iri, lamarin da ya sa Muhammadu Buhari ya tura tawaga don yi musu jaje.

Baya ga matsalar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriyar, jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna da Neja na fama da matsalar hare-haren ‘yan fashin daji da ke satar mutane don neman kudin fansa.

Sai dai hukumomin tsaron kasar sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shawo kan matsalar.

XS
SM
MD
LG