Accessibility links

Yau Juma'a 29 ga watan Mayu, Najeriya ta kafa sabon tarihi, bayan da aka rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo.

An rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban kasar bayan da ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a Abuja, babban birnin kasar a yau Juma’a, kuma shi ne shugaban kasar na farko da ya samu nasara akan shugaba mai ci.

Buhari zai jagoranci sabuwar gwamntin ne tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo a karkashin lemar jam’iyyar APC.

Sanye da farar riga Buhari ya kasance rike da Qur’ani a hanunsa na damaa lokacin bikin inda ya karbi rantsuwar cewa zai gudanar da ayyukansa cikin adalci tare da kare kasar.

Buhari ya karbi ragamar mulkin Najeriya ne yayin da kasar ke fama da matsalar tsaro a arewa maso gabashin kasar da satan mutane a kudanci da kuma matsalar cin hanci da rashawa.

Baya ga haka Buhari, mai shekaru 72, ya fara jagorantar kasar ne yayin da farashin mai ke faduwa a kasuwannin duniya har wa yau, yayin kuma da kasar ke yunkurin farfadowa daga matsalar rashin mai da aka fuskanta bayan wani yajin aiki da dallilaln mai suka yi.

Buhari dai ya taba mulkar Najeriyar a karkashin mulkin soja tsakanin shekarar 1983 da 1985.

Ga karin bayani a hirar Ibrahim Alfah Ahmed da Alhaji Kabiru Sani Abdullahi, wani tsohon mamba a kwamitin yakin neman zaben Muhammadu Buhar a filin dandalin VOA:

XS
SM
MD
LG