Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Rushe Kwamitin Binciken Cin Hanci Da Rashawa


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

A wani mataki mai kama da tauna tsakuwa da kuma ishara ga baragurbin jami'an gwamnati, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya rusa kwamitin binciken tafka almundahana saboda wani abu mai kama da baiwa kura ajiyar nama.

A kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ke yi na ganin an fuskanci alkibilar yaki da cin hanci da karbar rashawa gadan-gadan, gwamnati na daukar mataki kan zargin da ake wa shugabannin kwamitocin da ke yaki da cin hanci da rashawa.

Kwanannan Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya bada umarnin rushe kwamitin binciken cin hanci da rashawa da kwato dukiyoyi da kaddarorin gwamnati da aka sata nan take, wanda ke karkashin jagorancin Mista Okoi Obno Obla, wanda ake zargi da cin hanci da rashawa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin kasar da ya karbe ayyukan wannan kwamitin, sannan ya rusa shi, sannan ya tabbatar an kammala duk wasu bincike-bincike da aka fara ba tare da bata lokaci ba.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Umar Farouk Musa, daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG