Accessibility links

Buhari Ya Tafi Afrika Ta Kudu


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Lokacin Da Ya Kama Hanyar Tafiya Afrika ta Kudu jiya Asabar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya na Afrika ta Kudu inda ya je halartar taron koli na kasashen Afrika.

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari, ya tafi kasar Afrika ta kudu domin halartar taron koli na kasashen Afrika.

Wannna taro ya kasance na farko da Buhari ke halarta a karkashin inuwar kungiyar ta AU wacce ke gudanar da tarona jiko na 25, bayan da ya karbi mulkin kasar a watan jiya.

Babban batu a wannan taro ya kasance batu ne da ya shafi tsaro, wanda Najeriya ke fama da shi a yanzu haka.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Najeriya ta fitar ta ce shugaba Buhari zai gana da shugabannin kasashen Afrika a gefen taron kan batutuwan da suka hadin da kasashen domin yakar kungiyar Boko Haram.

A ranar Talata a ke sa ran Buhari zai dawo Najeriya bayan halartar wannan taro.

XS
SM
MD
LG