Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson murnar lashe zaben gama gari da aka gudanar a kasar.
Wata sanarwa da Malam Garba Shehu, kakakin Shugaba Buhari ya fitar, ta nuna cewa, "Birtaniya babbar kawa ce ga Najeriya, musamman idan aka yi la’akkari da yadda take taimakawa wannan gwamnati wajen kwato dukiyar Nakeriya da aka boye a kasar.
A cewar sanarwar, Shugaba Buhari na da burin ganin kasashen biyu sun ci gaba da karfafa dangantakarsu, musamman ta fuskokin cinikayya da tattalin arziki, matakin da zai taimakawa alu’momin kasashen biyu.
“Shugaban Najeriya, na mika sakon fatan alheri ga Firai Minista Johnson yayin da yake jagorantar al’umar Birtaniya a yunkurin ficewarta daga Tarayyar Turai,” sanarwar ta ce.
Nasarar wannan zaben wanda aka yi a jiya Alhamis, na nufin jam’iyya mai mulki ta Conservative ta zama mai rinjaye a majalisar dokokin kasar.
Gabanin zaben, jam’iyyar adawa ta Labor ce ke da rinjaye.
Wannan kuma wata matakala ce da Johnson zai yi amfani da ita wajen sake mayar da tsarin da ya gabatar wa majalisar kasar a baya kan yadda kasar za ta fice daga tarayyar ta EU, amma majalisar ta ki amincewa da ita a lokacin.
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 10, 2023
Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban CBN