Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi wa Paparoma Francis Fatan Samun Sauki


Paparoma Francis a fadar Vatican

Shugaban Najeriya ya yi kira ga daukacin ‘yan kasar da sauran al’umar duniya da su taya Paparoma da addu’a.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon fatan alheri ga shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Farncis, wanda aka yi wa tiyata.

Ofishin yada labarai a Fadar Vatican ya bayyana a ranar Lahadi cewa, an kwantar da Paparoma Francis a asibitin Gemilli Policinic da ke birnin Rome don a yi masa aiki kan wata lalura da ta shafi hanji.

“Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura sakon fatan samun sauki ga Shugaban Cocin Darikar Katolika, Paparoma Francis yayin da za a yi masa aiki a hanji.” Kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya fada cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Sanarwar ta kara da cewa, shugaban Najeriya ya yi kira ga daukacin ‘yan kasar da sauran al’umar duniya da su taya Paparoma da addu’a.

“Muna yi masa fatan samun sauki cikin sauri.” Sanarwa ta kara da cewa.

Gabanin ya je asibitin, Paparoma Francis mai shekara 84, ya jagoranci wani taron addu’a a St. Peter’s Square kamar yadda saba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG