Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Zai Je London Taro, Daga Nan Zai Duba Lafiyarsa


Shugaba Buhari

Fadar shugaban kasar ta ce cikin mako na biyu na watan Agusta shugaba Buhari zai koma Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi London don halartar taron koli kan bunkasa sha’anin ilimin kananan yara wanda ake fatan zai samar da kudade da kulla alaka tsakanin kasashen duniya wajen cimma wannan buri.

Wata sanarwa da kakakin Buhari Femi Adesina ya fitar a ranar Litinin ce ta bayyana wannan balaguro da shugaban zai yi a ranar Litinin, wanda har ila yau ta ce zai tsaya a birnin na London don duba lafiyarsa.

“Bayan taron kolin, shugaban zai kwashe wasu ‘yan kwanaki don duba lafiyarsa kamar yadda aka shirya zai yi tun a baya. Zai dawo cikin mako na biyu a watan Agustan 2021.” Sanarwar ta ce.

A ranar 24 ga watan Yuni fadar shugaban kasar ta sanar da cewa Buhari zai je kasar ta Burtaniya don duba lafiyarsa, sai dai sa’o’i kafin ya tafi aka dage ziyarar. Fadar shugaban kasar ba ta bayyana dalilin soke tafiyar ba.

A shekarun baya, shugaban na Najeriya ya kan je a duba lafiyarsa, illa a bara da bai je ba, saboda annobar COVID-19 da ta karade duniya, ta kuma sa aka rufe hanyoyin tafiye-tafiye.

Lokaci na karshe da Buhari ya je duba lafiyarsa a London shi ne a watan Maris din 2021.

Shi dai taron kolin da Buhari zai halarta, zai ba shugabannin kasashe damar su yi alkawarin tallafawa fannin ilimi don a bunkasa shi a kasashe da yankuna 90 a sassan duniya.

Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, Ministan ilimi Chukwuemak Nwajiuba, mai ba da shawara kan tsaron kasa Manjo-Janar Babagana Monguno mai ritaya da kuma Darektan hukumar tattara bayanan sirri Amb. Ahmed Rufai Abubakar.

XS
SM
MD
LG