Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bunkasar Tattalin Arziki: “Ba Mu Gani Ba A Kar”


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Rahoton fara farfadowar tattalin arzikin Najeriya, wanda ya kamata ya zama abin farin ciki ga 'yan Najeriya, baya ga zama abin faranta rai, ya kuma zama abin cece-kuce tsakanin jami'an gwamnati a gefe guda da kuma kwararru da talakawa a daya gefen.

Kamar yadda aka zata tun farko, ” masana tattalin arziki da kuma talakawa a Najeriya” kamar yadda wakinmu Ibrahim Abdul’aiziz ya kalato, “ na cigaba da maida martani game da rahoton da hukumar kiddigar tattalin arziki ta kasar ta fitar na cewa komadar tattalin arzikin kasar ya taso biyo bayan saukar farashin kayakin masarufi a kasuwanni da kuwa wasu aljaluman da kwararru su ka kafa hujja da su.

“Wasu talakawa ‘yan rabbana ka wadata mu a jihohin Adamawa da Taraba sun bayyana halin kuncin rayuwar da ake ciki, a yayin da ko a bangare guda hukumar kididdigar tattalin arziki ta NBS ke zakewa cewa a yanzu kasar ta tasam ma mikewa ta fuskar tattalin arziki. Talakawan su ka ce bas u gani ba a kar, (wai an ce ma kare ana buki a gidanku).

“To sai dai kuma yayin da hukumomi ke bada wannan tabbacin, baya ga talakawa, su ma masana tattalin arziki na ganin da sauran rina a kaba. Hon.Abdullahi Prembe tsohon kwamishina kuma masanin tattalin a jihar Adamawa, ya bayyana yadda suke kallon wannan batu a yanzu.

Ga dai wakilnmu Ibrahim Abdul’azi da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG