Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukina Faso: Za a Yi Zabe 22 Ga Watan Nuwamba


Wani dan kasar Burkina Faso yana kada kuri'arsa, lahadi 21 Nuwamba 2010 a Ouagadougou, babban birnin kasar.

Masu shiga tsakani a Afirka Ta Tsakiya sun bayyana wani shiri jiya Lahadi, na kawo karshen tashe- tashen hankulan Burkino Faso, inda aka kaddamar da wani juyin mulkin soji a makon jiya, da ya hambarar da gwamnatin wucin gadi ta farar hula.

Wannan shirin ya tanaji maido da gwamnatin farar hular, to amma ya kuma tanaji afuwa ga jagororin juyin mulkin.

Zabukan Shugaban kasa da na Majalisar Tarayya, Wadanda a baya aka tsaida ranar 11 ga watan Oktoba don gudanarwa, a yanzu za a gudanar ne a wani lokaci gabanin ran 22 ga watan Nuwamba.

'Yan takarar da ke dasawa da tsohon Shugaba Blaise Compaore, wadanda aka haramta masu shiga zaben na Oktoba, yanzu za a barsu su shiga.

Za a gabatar da wannan shawarar ga babban taron kungiyar Tarayyar Afirka gobe Talata don amincewa.

Janar Gilbert Diendere na rundunar dogarawan tsaron Fadar Shugaban kasa ne ya jagoranci juyin mulkin na makon jiya.

Ya hasala ne da yadda aka haramta ma magoya bayan Compaore shiga zaben.

Dogarawan tsaron sun tsare Shugaban wuccin gadi Michel Kafando da Firayim Ministansa da wasu Ministoci na tsawon wani dan lokaci.

Zanga zangar kyamar juyin mulkin ta rikide zuwa ta tashin hankali, inda aka kashe mutane akalla 10, baya ga raunata wasu sama da 100.

Compaore ya mulki Burkina Faso na tsawon shekaru 27, kafin aka hambarar da shi a wata zanga zangar da ta wanzu bara, bayan da ya yi yunkurin kwaskware kundin tsarin mulki don yin tazarce.

XS
SM
MD
LG