Accessibility links

Kasar Burtaniya ta bude gasar Olympic na 2012 yau Jumma’a, da bukukuwan

Kasar Burtaniya ta bude gasar Olympic na 2012 yau Jumma’a, da bukukuwan da su ka hada da shawagin jiragen yaki samfurin jet, da wasannin hasken wuta, da kuma tarihin wannan gasar kama daga 1896 zuwa lokacin da aka fara gasannin zamani har wannan lokacin.

‘Yan kallo wajen 60,000 ne su ka kalli saukar madadin Sarauniya Elizabeth ta Ingila, ‘yar shekaru 86 ta laimar sama jannati, a dandalin wasannin na Olympic tare da tauraron fina-finan nan da ya zama “James Bond” a shahararren fim din nan na Burtaniya na Dan Leken Asiri.

Jim kadan sai ita ainihin Sarauniyar ta mike a hankali a sa’ilinda da wata kungiyar waka ta yara ta raira mata waka mai taken, “Allah Shi Ja Zamanin Sarauniya.”

Jerin gwanon da aka saba na kasashe ya hada da akasarin ‘yan wasa sama da dubu goma da ke wurin, wadanda su ka yi ta maci a bayan tutocin kasashensu 204 da su ka shiga gasar.

Gasar da za a yi kwanaki 17 ana yi a fannonin wasanni 26, za a fara ta ne a yau Asabar zuwa ran 17 ga watan Agusta.

Miliyoyin ‘yan Burtaniya sun yi cunkus a wuraren kallo tare da abokai da ‘yan’uwa don kallo wannan harka ta wasannin motsa jiki mafi girma a wannan zamanin.

Ana kyautata zaton wannan harka da ta lakume kudi dala miliyan 40, za ta nishadantar da ‘yan kallo wajen miliyan dubu a duniya.

XS
SM
MD
LG