Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burundi: Mutum Na 13 Ya Mutu


Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza

Sabon rikicin siyasar kasar Burundi ya kuma lakume ran mutum guda, yayin da masu zanga zanga da ke ci gaba da nuna adawa kan yunkurin da shugaba Pierre Nkurunziza ke yi na sake tsaya takara a zabe mai zuwa.

Rahotanni sun ce mutane uku har ila yau sun samu rauni a sabon rikicin.

Wadanda suka shaida lamarin da jami’an kungiyar ba da agaji ta Red Cross, sun ce sabon rikicin ya barke ne a yau Alhamis bayan da ‘yan sanda suka yi yunkurin shiga tsakanin magoya bayan shugaban kasar da masu adawa da shi a Bujumbura, babban birnin kasar.

A wannan makon kotun kundin tsarin mulkin kasar ta Burundi, ta yanke hukuncin cewa shugaban na da damar ya sake tsayawa takara a wa’adi na uku, lamarin da ya harzuka ‘yan adawan, wadanda suka ce hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

A jiya Laraba shugaba Nkurunziza ya sha alwashin cewa idan har aka zabe shi a karo na uku, ba zai sake tsayawa takara ba.

Ya kuma yi kira ga masu zanga zangar da su kawo karshen boren da su ke yi, yana mai cewa yana mai cewa akwai muhimmanci a gudanar da zaben na 26 ga watan Yuni cikin lumana.

Ya zuwa yanzu, akalla mutane 13 suka rasa rayukansu tun bayan barkewar zanga zangar a ranar 26 ga watan Aprilu, wato ranar da Mr. Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG