Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burundi Ta Hana VOA Da BBC Gabatarda Shirye Shiryen su Har Wata Shida.


Karenga Ramadhan, shugaban hukumar kula da kafofin yada labarai na Burundi

Burundi, ta bada sanarwar dakatar da shirye shiryen Muriyar Amurka(VOA) da BBC a kasar na tsawon wata shida, kasar ta dauki wannan matakin ne makonni biyu kamin 'yan kasar su kada kuri'ar raba gardama kan daftarin sauye sauye ga tsarin mulkin kasar da zai hada harda sashen da yayi magana kan kayyade wa'adin shugabancin kasar.

A jiya jumma'a ce majalisar kula da sadarwa ta kasar ta bada wannan snaarwar, ta zargi Muriyar Amurka da BBC da karya dokokin kasar dangane kafofin yada labarau, da kuma aikata ba daidai ba. Sanarwar tace umarnin zai fara aiki daga ranar Litinin.

Haka nan majalisar ta kuma ja kunnen tashar Radio ta Fararansa,((RFI)) a takaice, ta zargi tashar da yada labaran kariya cewa za'a farwa duk wadda ya kada kuri'ar rashin amincewa da sauye sauyen da ak shirin kada kuri'ar raba gardamar.

A cikin sanarwa da ta bayar kan wannan mataki, darektar Muriyar Amurka Amnadan Bennett, tayi Allah wadai da matakin da majalisar kula da kafofin yada labarai ta dauka, na hana wannan tasha gabatar da shirye shiryensa ga masu sauraro a kasar.

Amanda tace "masu sauraro suna dogaro akan tashar ta basu rahotanni na gaskiya, ba tareda son zuciya ba dangane da al'uma d a suke aukuwa kasar,saboda haka wannan mataki ya hana al'umar Burundi wata kafar yada labarau wacce take aiuki bil hakki da gaskiya.

Wani jami'i a ma'aikatar harokokin wajen Amurka yace "Amurka bata ji dadin wannan mataki da Burunidn ta dauka ma, kuma Amurkan ta gabatarwa gwamnnatin Burundi wannan damuwa kai tsaye.

Sanarwar tace masu sauraro za su iya cin gaba da kama wannan shirye shiryen mu ta gajeren zango, da kuma ta kan internet.

Kungiyar da take kare muradun 'yan jarida ta kasa da kasa ita ma ta soki lmirin wannan mataki, tana mai cewa babu wata manufa ta dakatar da tashoshin biyu, illa yunkurin gwamnatin kasar dake Gabashin Afirka ta ci gaba da sanya takunkumi kan kafofin yada labari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG