Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burundi Tace ba Zata ba Kotun Kasa da Kasa ICC Hadin Kai ba


Yan Kasar Burundi
Yan Kasar Burundi

Gwamnatin Burundi tace ba zata bada hadin kai ga kotun manyan laifukan ta kasa da kasa ta ICC a kan aniyarta na gudanar da bincike a kan zargin take hakkin bil adama a kasar.

Kasar dake Afrika ta Gabas ta fice daga yarjejeniyar kotun duniyar ta ICC amma kuma kotun tace ficewar ba zai hanata aiwatar da aikinta a cikin kasar a kan karar laifukar da aka gabatar mata a baya.


Da take jawabi ga manema labarai a babban birnin Burundi Bujumbura, Ministan shari’a Aimee Laurentine tace kotun ICC bata da hurumin gudanar da bincike a cikin kasarta.

Tace Burundi ba mamaban kotun ICC bane, kuma babu ruwanta da batun wata shawara da kotun zata dauka. Gwamnatin Burundi ba zata yi aiki da wata shawarar kotun ba kuma tana kara jaddada matsayanta cewar ba zata ba kotun ICC hadin kai ba kuma ba zata lamunta da aniyar Kotun na neman shiga kasar Burundi ta gudanar da aikinta bisa zalunci ba.


Martanin na gwamnati Burundin na zuwa ne kwana guda bayan da alkalai uku na Kotun ICC suka bada umarni ga mai shigar da kara da ya bude bincike a kan zargin take hakkin bil adama da aka yi a ciki da wajen kasar Burundi tsakanin Afrilun shekarar 2015 da kuma Oktoban shekarar 2017.


Burundi ta zama mamban yarjejeniyar Rome Statute wacce ta kafa kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC a shekarar 2004. Kasar ta bada sanarwar ficewarta daga wannan yarjejeniya a cikin watan Oktoban bara kuma snarwar ta fara aiki a watan da ya gabata. Burundi tana zargin kotun da auna kasashen Afrika.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG