WASHINGTON D.C. —
Tsohon Magajin Garin South Bend a jihar Indiana, Pete Buttigieg, ya hakura da fatansa na ganin ya zama Shugaban kasar Amurka a 2020.
Kwamitin yakin neman zaben Buttigieg ya sanar a jiya Lahadi cewa, ya janye daga neman jam’iyyar Democrat ta tsaida shi dan takarar shugabancin kasar.
Tsohon Magajin Garin ya yanke wannan shawara ce, bayan ya tashi ba wakili ko "delagate" ko daya a zaben fidda dan takara da aka gudanar a ranar Asabar a jihar South Carolina.
Buttigieg ya kara kaimi biyo bayan nasarar da ya yi da kyar a zaben jihar Iowa a watan da ya gabata, sannan kuma ya zama na biyu, daf da wanda ya zo na daya, a New Hampshire.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama
-
Fabrairu 22, 2021
COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka
-
Fabrairu 20, 2021
Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance
-
Fabrairu 17, 2021
Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka