Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

California: Wani Dan Bindiga Ya Kashe Mutum 3 A Garin Gilroy


Wani mahari ya hallaka mutum 3 tare da jikkata wasu mutum 15 a garin Gilroy na jihar California a wajan wani bikin da ake kira Garlic Festival.

Hukumomi a yammacin jihar California ta Amurka sun ce wani mahari ya kashe akalla mutum uku a jiya Lahadi da yamma a wajen wani biki da ake kira “Garlic Festival”

Harin ya faru ne a garin Gilroy, wanda ‘yan sanda suka ce maharin ya kai harin ne dauke da bindigogi.

Sannan wasu mutum 15 sun jikkata, amma babu wani tabbacin ko an harbe su ne.

A lokacin da harin ya auku, da ma Akwai ‘yan sanda a wurin bikin, kuma shugaban ‘yan sandan garin na Gilroy, Scot Smithee, ya ce sun yi sauri suka fafata da wanda ake zargi kuma suka harbe shi har lahira.

Smithee ya fadawa manema labarai jiya da daddare lokacin da ya ke masu dan takaitaccen bayani cewa wasu shaidu sun sanar da su cewa, ta yi wu akwai wani dan bindigar na biyu.

Amma ‘yan sanda har yanzu ba su tabbatar da hakan ba, kuma ko da akwai wani mutum na biyu, ba su san ta yaya suka hadu akan harin ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG