Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CAN Ta Dakatar Da Shugabanta Na Jihar Gombe Saboda Taya Pantami Murna


Kuniyar Kiristoci ta Najeriya CAN
Kuniyar Kiristoci ta Najeriya CAN

Takardar ta ci gaba da cewa matakin na shugaba Congo na taya Pantami murna, tamkar takala ne da raina shugabancin CAN na kasa, haka kuma ba ya wakiltar matsayar shugabannin kungiyar.

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN, ta dakatar da shugaban kungiyar na jihar Gombe Sunday Congo, sakamakon aikewa da takardar taya murna ga Ministan sadarwar zamani Dr. Isah Ali Pantami, akan ba shi matsayin Farfesa da jami’ar fasaha ta tarayya da ke Owerri ta yi.

A cikin takardar dakatarwar, sakataren kungiyar ta CAN, Joseph Daramola, ya bayyana cewa rubuta takardar taya Pantami murna da Congo ya yi a madadin kungiyar, ba tare da tuntubar shugabancin ta na kasa ba ya saba ka’ida.

Takardar ta ci gaba da cewa matakin na shugaba Congo na taya Pantami murna, tamkar takala ne da raina shugabancin CAN na kasa, haka kuma ba ya wakiltar matsayar shugabannin kungiyar.

Takardar dakatar da shugaban CAN na jihar Gombe
Takardar dakatar da shugaban CAN na jihar Gombe

A kan haka ta umarce shi da ya sauka daga mukaminsa, ya kuma hannunta dukkan lamurran kungiyar ga wanda ke bin sa a mukamin kungiyar a jihar ta Gombe.

Shugaban na CAN na jihar Gombe Sunday Congo, ya aike da takardar taya murna ga minista Pantami, inda ya ke jinjinawa kyawawan ayukansa, tare da bayyana shi a matsayin “da”.

Takardar taya murnar mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar na jihar Gombe Apostle John Adedigba, a madadin kwamitin rikon kwarya na kungiyar na jihar, ta bayyana cewa Pantami ya sami nasarori da dama a matsayin da yake rike da shi yanzu haka, inda kuma ta kara da cewa “suna alfahari da shi.”

Sunday Congo dai ya tabbatarwa da jaridar The Guardian cewa ya sami takardar dakatar da shi a yayin da yake kan tafiya a wajen jihar, kuma zai bayyana matsayarsa kan lamarin idan ya dawo daga tafiyar.

Wannan lamari kuma na ci gaba da haifar da martani da ra’ayoyi daban-daban a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta na yanar gizo.

XS
SM
MD
LG