Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canada Za Ta Kara Yawan Bakin Haure Da Take Mayarwa Kasarsu


wadansu masu neman mafaka
wadansu masu neman mafaka

Hukumar dake kula da bakin iyakar kasar Canada na shirin ‘kara yawan bakin hauren da take mayarwa kasashensu wadanda suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba zuwa 10,000 a wannan shekarar.

Wannan ya hada da bawai kawai ‘yan gudun hijirar da basu sami karbuwa ba da masu neman mafaka, amma har da wadanda jami’ai ke kallonsu a matsayin barazana ga kasa.

A lokacin da maigana da yawun hukumar dake kula da bakin iyaka ta Canada yake magana da kafar labaran kasar, ya ce “yayin da Canada ta shafe shekaru tana karba da maraba da bakin haure da masu neman mafaka, ana bukatar duk wandada suka shiga kasarmu su kiyaye dokar kasar.”

Yanzu haka akwai bakin haure kusan 18,000 da ake shirin mayar da su kasashensu, 5,300 daga cikinsu babu wani abu da zasu iya yi a barsu a kasar, dole sai an mayar da su.

‘Yan hamayya masu ra’ayin mazan jiya a kasar sun kira yawan bakin hauren dake tsallaka iyaka suna shiga Canada a matsayin rikici. Suna mai cewa gwamnati bata da wani shiri na daukar batun da muhimmanci.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG