Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Dubu 700 Ne Daga Kasashe Goma Suka Wuce Wa'adin Bizarsu Ta Shigowa Amurka


Kirstjen Nielsen, Sakatariyar Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka
Kirstjen Nielsen, Sakatariyar Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka

Wasu alkalumma da ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta fitar sun nuna cikin watanni 12 daga watan Oktoban shekarar 2016 zuwa watan Satumban shekarar 2017 mutane dubu 700 da suka shigo kasar daga kasashe goma suka wuce wa'adin bizarsu

Hukumar tsaron cikin gida ta Amurka da ake kira Homeland Security, ta ce sama da ‘yan kasar waje dubu 700 da ya kamata su fita daga Amurka ne suka wuce wa’adin da aka diba musu na watanni 12 a takardun v

bizarsu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito.

Shi dai Shugaba Donald Trump, ya fi mayar da hankali ne kan gina katanga tsakanin kasar da Mexico, wacce za a kashe biliyoyin daloli.

Amma kuma sabuwar kididdiga, wacce ake fitawar a duk shekara, ta nuna yadda bakin da visarsu ta kare, suke zama babban sanadin karuwar mutanen da suke zaune a Amurka ba tare da izni ba.

Daga watan Oktoban 2016 zuwa watan Satumbar 2017, an samu mutum dubu dari-bakwai-da-daya -da-dari-tara, da suka shigo Amurka ta jirgin sama ko na ruwa, wadanda bizarsu ta wuce wa’adinta, adadin da ya haura yawan jama’ar jihar Vermont ko kuma Wyoming.

'Yan Canada ne suka fi kowacce kasa yawan wadanda bizarsu ta kare da suka ki fita, sai Mexico dake biye da ita, sai Venezuela, sannan sai Birtaniya yayin da Colombia ke biye da ita, sannan sai Najeriya sai China da Faransa da Spain da kuma Jamus wacce ta cike adadin kasashe goma, da 'yayansu suke zarce wa'adin bizarsu a Amurka.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG