Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Carlo Ancelotti Ya Sake Zama Kocin Real Madrid


Carlo Ancelotti (Shafin yanar gizo)
Carlo Ancelotti (Shafin yanar gizo)

Wannan shi ne karo na biyu da Ancelotti dan asalin kasar Italiya mai shekara 61, zai horar da ‘yan wasan na Madrid.

Real Madrid ta nada Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocin kungiyar.

Hakan na nufin Ancelotti wanda ya taba horar da ‘yan wasan na Real Madrid, shi ya maye gurbin Zinedane Zidane.

Zai zauna a kungiyar har zuwa tsawon kakar wasa uku. An kuma dakko shi ne daga Everton.

A karshen makon da ya gabata Zidane ya ajiye aikinsa na horar da ‘Yan wasan Madrid.

Wannan shi ne karo na biyu da Ancelotti dan asalin kasar Italiya mai shekara 61, zai horar da ‘yan wasan Madrid.

Karin bayani akan: Carlo Ancelotti, Zinedane Zidane, Everton FC da Real Madrid.

Ya horar da su a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015 inda har ya lashe kofin zakarun turai.

“Ina so na mika godiyata ga Everton FC, ‘yan wasa da masu goyon bayan kungiyar bisa damar da suka ba ni, na horar da wannan babbar kungiya mai cike da tarihi.” Ancelotti wanda shi ne kocin Everton ta Ingila, ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya kara da cewa, “na yanke shawarar tafiye ne, saboda babban kalubalen da ke gaba, a wannan kungiya wacce a kowane lokaci tana zuciyata.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG