Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ce-Ce-Ku-Cen Trump Da Gwamna Cuomo


Gwamnan New York, Andrew Cuomo

Gwamnan New York ya mayar wa da Shugaban Amurka Donald Trump martini kan ko jihar ta nemi tallafi fiye da kima wajen yaki da cutar coronavirus.

Yayin da yake gabatar da taron manema labarai da yake yi a kullum, gwamna Andrew Coumo, ya mayar wa da Trump martini kan wasu sakonnin Twitter biyu da ya wallafa a lokacin yana gabatar ta taron manema labaran.

A daya daga cikin sakonnin, Trump ya kalubalanci gwamnan na New York wanda dan Democrat ne, da ya tsaya ya yi “aiki” ya dena yawan “korafi.”

“Mun samar da dubban gadajen kwanciya a asibiti da ba a bukata ko kuma ba a yi amfani da su ba,” Trump ya ce.

A sako na biyu kuma, Trump ya ce, “mun ba New York kudade masu yawa da kayayyaki fiye da sauran jihohi,” yana mai cewa gwamnan “ko godiya bai ya yi.”

Sai dai gwamna Cuomo ya mayar da martini ga shugaban na Amurka.

“Da farko, idan yana zaune ne a gida yana kallon talbijin, ina ga ya kamata ya mike ya je ya yi aiki.” In ji Cuomo.

Ya kuma kare kansa inda ya ce, ya sha mika godiyarsa ga Trump saboda tallafin da gwamnatin tarayya ta ba jihar, ciki har da gina asibiti mai gadaje 2,500 tare da aikawa da jirgin ruwan sojin kasar mai dauke da asibiti, wato Comfort.

“Saboda haka, ban san me ake so na yi ba, na aika mai da furanni?” Cuomo ya ce.

New York dai ita ce jihar da cutar coronavirus ta fi kamari, inda ya zuwa ranar Juma’a, sama da mutum 223,000 aka tabbatar suna dauke da cutar.

Sannan mutum kusan 13,000 sun mutu a asibitoci sanadiyyar ta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG