Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cece-Kuce Kan Zaben Shugabannin Jam'iyyar APC


Wani taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar ta Cross Rivers (Facebook/ Benedict Ayade)
Wani taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar ta Cross Rivers (Facebook/ Benedict Ayade)

A yayin da jam'iyyar APC za ta fara zaben Shugabannin ta a matakai daban-daban a ranar Assabar, ana ci gaba da cece-kuce da saka ayar tambaya akan Halacci da hurumin kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar na shirya taron.

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shirya soma gudanar da zaben sabbin shugabanninta, tare da farawa daga matakin gundumomi a gobe Asabar.

Wannan matakin shirya zabukan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kiraye-kirayen a binciki halacci kwamatin tsara taron na kasa a bisa hurumin doka, bayan yanke hukuncin raba gardama da kotun kolin kasar ta yi a ranar Laraba, wacce ta ba gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu nasara.

Furucin da 3 daga cikin masu shari’a 7 na kotun kolin kasar suka yi kan cancantar kwamitin riko na jam’iyyar APC karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya haifar da cece-kuce tsakanin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

Haka kuma wannan ya sa wasu mambobin suka yi kira ga gwamnan da ya ajiye aikin rikon kwaryar domin ceto jam'iyyar daga yiyuwar rugujewa.

Idan ana iya tunawa, a 'yan kwanakin baya-bayan nan karamin ministan kwadago da nagartar aiki, Festus Keyamo, ya gargadi jam’iyyar APC da ta dakatar da batun gudanar da zabukan shugabanninta daga matakin gundumomi zuwa sama da ta shirya yi, ya na mai cewa gudanar da taron zabukan zai iya zama mara tasiri idan aka kalubalanci hakan a gaban kotu.

Mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin siyasa sanata Babafemi Ojudu, da kuma na kan harkokin yankin Neja Delta, Ita Enang, sun umarci jam’iyyar APC da ta mutunta umarnin manyan lauyoyin kotun koli domin abun da kan iya tasowa na kalubalantarsa a kotu.

Saidai, wasu jiga-jigan lauyoyi a jam’iyya ciki har da mataimakin shugaban majalisar dattawa, sanata Ovie Omo-Agege, sun ce kwamitin da Mai Mala Buni ke jagoranta halattace ne, kuma babu wani hukuncin kotu da zai iya shafar sa yanzu, ko kuma nan gaba.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni

Idan ana iya tunawa, an kafa kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC ne a watan Yunin shekarar 2020, biyo bayan rusa kwamitin gudanarwar APC na Kasa wato da kwamared Adams Oshiomhole ya jagoranta da kotu tayi a lokacin, bisa zargin yin amfani da mukami ba bisa ka'ida ba.

Duk da cece-kuce da ake yi kan halaccin kwamitin riko da Mai Mala Buni ke jagoranta, babban sakataren kwamitin rikon na APC, Sanata John James Akpanudoedehe, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis, ya ce jam’iyyar APC zata fara taron zaben shugabannin ta daga matakin gundumomi a gobe asabar.

Shi ma mataimaki na musamman ga gwamna Babagana Umara Zullum na jihar Borno kan harkokin cinikayya da zuba jari, Barista Bashir Maidugu, ya bayyana cewa, kamata ya yi a gudanar da babban taron jam’iyyar APC kafin zabukan shuwagabannin jam’iyyar wadanda za su gudanar da zabukan gabanin babban zaben shekarar 2023.

XS
SM
MD
LG