Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Charles Taylor Zai Yi Zaman Kaso Har Shekaru 50.


Tsohon shugaban Laberiya Charles Taylor kamin a yanke masa hukunci laraban nan.

Wata kotun musamman ta yanke hukuncin daurin shekaru 50 a kurkuku ga tsohon shugaban kasar Laberiya Charles Taylor saboda laifuffukan yaki da kuma wasu laifuffukan cin zarafin bil Adama.

Wata kotun musamman ta yanke hukuncin daurin shekaru 50 a kurkuku ga tsohon shugaban kasar Laberiya Charles Taylor saboda laifuffukan yaki da kuma wasu laifuffukan cin zarafin bil Adama.

A yau Laraba kotun ta musamman ta gabatar da hukuncin a birnin Hague, ta ce Taylor ya yi amfani da mukamin sa ya taimakawa ‘yan tawaye sun karya doka maimakon ya bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Alkalin da ya shugabanci zaman yanke hukuncin, Richard Lussick, ya ce baiwa ‘yan tawaye makamai da shawarwari da kuma karfafa mu su guiwa su ne abubuwan da su ka kara dulmuya Charles Taylor kuma su ka kara nuna tsananin laifin da ya aikata.

Masu shigar da kara sun bukaci a yi masa daurin shekaru tamanin a kurkuku, amma sai kotun ta ce shekarun tamanin za su wuce kima.

A watan jiya kotun ta samu Taylor dan shekaru sittin da hudu, da aikata dukkanin laifuffuka goma sha daya da su ka hada da kisan kai, da fyade, da mayar da mata bayin da ake yin lalata da su, da sa yara aikin soja, da kuma bautarwa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG