Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Za Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa


Shugaban kasar China Xi Jinping
Shugaban kasar China Xi Jinping

Gwamnatin Kasar China tace zata kaddamar da wani sabon tsarin Yaki da cin hanci da rashawa mai karfi a Beijing babban birnin kasar, da kuma yankunan Shanxi da Zhejiang.

Jami’ai sunce an shirya sabon tsarin ne ya zama mai zaman kansa, da zai kunshi hukumomin sa ido da zasu rika sawa masu rike da mukaman gwamnati ido da suka hada da fannin harkokin shari'a.

Wadansu masu sa’ido kan lamura sun yaba kirkiro da sabon tsarin, da suka bayyana a matsayin tsarin cigaba da zai kara martaba da kuma kasancewar tsarin sa ido mai cikakken iko . Wasu kuma suna shakkun hukumar zata iya zama mai zaman kanta ba ta raeda Jam’iyyar tayi katsalandan a harkokinta ba, suna kuma bayyana fargaban cewa, irin ikon fada aji da jam'iyar ke da shi zai iya kara yawan Cin hanci da rashawa.

Ranar Lahadi wani kwamitin Jam’iyyar National People's Congress- NPC, ya amince da tsarin garambawul din na farko da nufin maida tsarin sa ido na hukumar ta kasa waje guda da nufin shawo kan albazaranci da ya yi katutu a kasar. .

A karkashin shirin Kwamitin da ke kula da shirin zai kafa Babban Ofishi da kuma na kananan hukumomi wanda zai dinga bada bayanai ga jam'iyar NPC. Zasu kasan ce masu zaman kansu sannan na kananan hukumomi, bangaren shari’a zasu rika tsamo reshe reshe domin samar da bincike akan jami’an dake rike da ofisoshi a kasa baki daya.

XS
SM
MD
LG