Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ce Take Kama Kifi A Kogunan Yammacin Afirka


jiragen masunta.
jiragen masunta.

Sannan ta kai shi kasarta ko wasu manyan kasashen duniya.

A kullu yaumi, jiragen masunta daga kasashen waje, yawancinsu daga kasar China suna shawagi da nufin kama kifi a kan tekun Afrika ta yamma. Suna kama miliyoyn kifi, abin da ya kamata masunta yankin su kama. Ana aika kifin zuwa China da Turai da ma Amurka don biyan bukatun abincin da ake samarwa daga teku da habbaka masana’antun biliyoyin daloli na wadannan kasashe.

Wadannan jiragen ruwan masunta kasashen waje suna kawo kuncin rayuwa ga masunta wannan yanki kamar yanda wakilin Muryar Amurka Ricci Shryock ya tattara bayana na musamman a watan da ya gabata.

Masuntan daga Asia da Turai suna kassarar tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma na ayyuakn yi dubu dari uku da kudaden shiga dala biliyan biyu a cewar John Hoceyer, wani masanin albarkatun cikin ruwa dake tare da Kungiyar kula da harkokin Muhalli mai zaman kanta ta Greenpeace.
Masana da jami'ai sun raasa sani irin matakan da zasu dauka domin shawo kann wannan al'amari

Masu kamun kifi daga China suna bulaguro zuwa Afrika saboda kifi a yankinsu ya kusan karewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG