Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Na Shirin Barin Shugaban Kasa Ci Gaba Da Mulki Har Iyakar Rayuwarsa


Xi Jinping shugaban China na iya ci gaba da mulki har iyakar rayuwarsa

Mahukumtan China na shirin wani kuduri da zai bar shugaban kasa ci gaba da mulki har iyakar tsawon ransa lamarin da Fadar White House ta Amurka ta ce wannan shawarar ta rage ga mahukumtar kasar ta China amma Shugaba Trump yana goyon bayan shirin takaita wa'adin shugaban kasa a nan Amurka

Fadar White House tace shirin da China take yi na janye wa’adin mulkin shugaban kasa, wani yunkurin da zai ba shugaba Xi Jinping ikon ci gaba da mulkin kasar har iya rayuwarshi, batu ne na cikin gida da ya shafi China ita kadai.

"Ina jin wannan shawara ce da China zata yanke bisa radin kanta, yadda taga yafi dacewa da kasarta" bisa ga cewar kakakin fadar White House Sarah Huckabee Sanders yayin ganawa da manema labarai jiya.

Wa’adin mulki abu ne da Trump yake goyon baya a nan Amurka, amma wannan batu ne da China zata yankewa kanta hukumci a kai, in ji ta.

Jam’iyyar kwaminis ta kasar China ta bada shawarar cire wa’adi biyu kan mulki na shugaban kasa daga kundin tsarin mulkin kasar, bisa ga rahotannin da kafofin sadarwa suka yayata ranar Lahadi.

Wannan zai karawa shugaba Xi karfi wanda tuni ake daukarsa a matsayin shugaban kasar China mafi tasiri a cikin shekaru da dama.

Jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya yabi Xi, tare da cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsu, kuma yana matukar ganin kimar shugaban na China.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG