Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Kira A Tsagaita Wuta A Syria


Antonio Guterres, sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Saboda mutane fiye da dubu dari hudu da suke cikin mawuyacin hali a yankin Ghouta kasar Syria, sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi hukumar sulhu ta majalisar ta amince da kudurin tsagaita wuta a yakin Syria na tsawon kwanaki 30

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Antonio Guterres yana kira ga kwamitin sulhu ya amince da kudurin tsagaita wuta na tsawon kwanaki talatin ba tare da bata lokaci ba a Syria domin a taimakawa kimanin mutane dubu dari hudu dake yankin Ghouta da ya ce “suna cikin matsanancin halin kunci”

Guterres ya ce, na hakikanta cewa, gabashin Ghouta ta gagara” ya ce “kirana ga dukan wadanda ke tashin hankalin shine su daina yaki ba tare da bata lokaci ba a gabashin Ghouta domin a iya kai kayan agaji ga mabukata.

Shekarar da ta gabata,aka ayyana yankin a matsayin daya daga cikin wuraren da za a daina tada hankali a wata yarejejeniya da aka cimma da magoya bayan Syria, Rasha da Iran da kuma Turkiya.

Sai dai an ci gaba da fada kwanan nan yayinda sojojin Syria da abokan kawancenta suka nuna alamar kaddamar da harin da nufin sake kwace yankin da ya kasance daya daga cikin yankunan da suka rage kusa da Damascus a hannun mayakan kungiyar hamayya.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG