Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Dauki Tsatstsauran Mataki Kan Yara Da Suke Buga Wasan Bidiyo


China ta kirkiro wani sabon tsari na takaita tsawon lokacin da kananan yara za su rika yi suna wasan wasa kwakwalwa da ake kira Video Games a harshen ingilishi.

Hukumomin kasar sun jima suna dora laifi akan yawan mu’amulla da video game da yaran kasar ke yi, a matsayin abin da ke kashewa yara karfin ido ya kuma sa su fadi a jarabawa a makaranta.

Daga yanzu, duk yaron da bai kai shekaru 18 ba, ba zai rika buga wasan na video game ba daga karfe goman-dare zuwa takwas na safe agogon yankin, sannan minti casa’in kawai za su rika yi kullum a tsakanin ranakun Litinin zuwa Juma’a, sannan a karshen mako da ranar da ake hutu, za su rika wasan na tsawon sa’o’i uku ne kawai.

China dai na daya daga cikin kasashen da kasuwar wasanni video game ke ja a duniya, inda ta kan samu kudaden shiga har dalar Amurka biliyan 33 a duk shekara.

Facebook Forum

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG