WASHINGTON D C —
A birnin Beirut, dubban mutane ne suka fito yau Lahadi don nuna goyon bayansu ga shugaban kasar Lebanon.
Jama’ar sun gudanar da gangamin ne a kusa da fadar shugaba Michel Aoun dake kudu maso gabashin birnin Beirut.
Nuna goyon bayan ga Aoun na nuna adawa da zanga zangar da wasu ‘yan Lebanon suka fara a fadin karamar kasar dake yankin tekun bahar rum a watan da ya gabata, suna neman a yi garambawul a siyasar kasar da ake nuna wariya.
Masu zanga zangar sun kuma dora laifin cin hanci da rashawa da suka yi yawa sosai, da kuma rashin ayyukan raya al’umma akan gwamnatin kasar.
Ko da yake, ana sa ran gudanar da zanga zangar kin jinin gwamnati yau Lahadi da yamma a tsakiyar birnin Beirut.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 26, 2023
Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris Ta Isa Ghana
-
Maris 21, 2023
Saudiyya Ta Ce Ranar Alhamis Watan Azumi Zai Kama
-
Maris 17, 2023
Kotun ICC Ta Ba Da Izinin Kama Putin
-
Maris 13, 2023
Shugaba Buhari Ya Taya Xi Jinping Murnar Sake Lashe Zabe
Facebook Forum