Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Kara Harajin Da Ya Kai Dala Biliyan 50 Akan Kaya Daga Amurka


Tashar jirgin ruwan Yangshan, Shanghai cike da kaya daga Amurka
Tashar jirgin ruwan Yangshan, Shanghai cike da kaya daga Amurka

Karin harajin da China ta sanar jiya Laraba martani ne akan abun da Amurka ta yiwa kayanta dake shigowa Amurka kuma ta ce matakin zai fara aiki ne ranar da Amurka ta fara aiki da nata

A jiya Laraba Sin, ko China, ta bayyana anniyarta na kara kudin fito ko haraji da yakai dala biliyan 50 akan kayayyakin da za a shigo dasu daga Amurka, a zaman martani kan irin wannan mataki da Amurka ta dauka kan kayayyaki daga kasar.

Wannan matakin dai zai kara kudin fito da kashi 25 akan kayayyakin Amurka har 106, da suka hada da waken Soya, da Jirgin Sama da motoci.

Maaikatar Ciniki da masana’antu ta kasar ta China ta dauki wannan matakin ne dai kasa da Sa’o’i 11 bayan da Amurka ta bayyana kudirin ta akan kayayyakin kasar China.

Sai dai ma’aikatar tace batun ko yaushe wannan sabon harajin zai fara aiki ya dogara ne akan ranar da na Amurka ya fara aiki da sabon harajin da ta bayyana.

Yiyuwar rikici ta fuskar kasuwanci tsakanin kasashen biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya ya tada hankalin masu zuba jari, domin haka ne ma kasuwar hannayen jari ta Amurka ta fara hada-hadar a wunin jiya da faduwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG