Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Shiga Mataki Na 2 Na Gwajin Allurar Rigakafin Coronavirus


Kasar China ta shiga mataki na biyu na gwajin allurar rigakafin Coronavirus, da ta ke yi kan mutum 500 ‘yan sa kai, da aka samo daga birnin Wuhan, inda aka fara samun bullar annobar.

Wannan shi ne karon farko a mataki na biyu da za a gwada allurar rigakafin COVID-19 kan bil’adama, a yunkurin da ake a fadin duniya na samun maganin annobar, a cewar kamfanin dillancin labarai a kasar, Xinhua.

China dai ta kammala matakin farko a karshen watan Maris, inda ta yi amfani da mutum ‘yan sa kai 108.

Wadanda baki dayansu yanzu haka an sallamesu daga asibitin da aka gudanar da gwajin, kuma dukkanninsu an bada rahoton cewa suna cikin koshin lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG