Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Takaita Yawan Man Da Ta Ke Sayar wa Korea Ta Arewa


Shugaban China Xi Jingping, a taron kungiyra BRICS, ranar Tuesday, Satumba 5, 2017.

A wani mataki na fara aiwatar da matsayar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya dauka kan karin takunkumi akan Korea ta arewa, China ta fara takaita huldodin kasuwancinta da Korea ta arewan.

A yau Asabar, China ta sanar cewa ta takaita safarar shigar da man fetur zuwa cikin Korea ta Arewa, a wani mataki na bin umurnin kwamaitin sulhu Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya saka mata karin takunkumi kan shirinta na gina makamin nukiliya.

A wata sanarwa da ma’aikatar hadahadar kasuwancin kasar ta Sin ta wallafa a shafinta na yanar gizo, kasar ta Sin ta ce za a rika shigar da tacaccen gangan man fetur miliyan biyu ne cikin kacal a shekara, kuma wannan sabon tsari zai fara aiki ne ranar daya ga watan Oktoba.

Amma ma’aikatar ta ce ta dakatar da safarar tsurar man gas nan take.

Shi dai kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin duniya ya haramta yin amfani da man fetur da sauran dangoginsa wajen shirin hada makamin nukiliyan na Korea ta arewa, a cewar sanarwar.

A can baya, kasar ta China ta kan goyi bayan Korea ta arewa kan wasu al’amura, amma a kullum ta na kara nuna rashin gamsuwarta kan yadda gwamnatin Kim Jong Un ke tafiyar da kasar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG