Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Duniya Sun Fara Hallara a Babban Taron MDD


Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York
Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York

Shugabannin duniya na shirin taruwa a birnin New York da ke Amurka, domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ake sa ran batun gwajin makamin nukiliyan Korea ta Arewa shi zai mamaye batutuwan da za a tattauna a kai.

Gobe Litinin ake sa ran shugabannin duniya za su hallara a birnin New York domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

Wannan shi ne karon farko da shugaban Amurka Donald Trump zai halarci taron, yayin da ake hasashen batun shirin nukiliyan Korea ta arewa, shi zai mamaye zantukan da za a tattauna.

A farkon makon da ya gabata, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da karin wasu sabbin tsauraran takunkumi akan hukumomin Pongyang.

Takunkumin baya-bayan nan shi ne na biyu a jerin makwanni biyar, wadanda aka saka su a matsayin martani saboda gwajin abinda ake kyautata zaton makamin hydrogen bom ne da Korea ta arewan ta yi a ranar uku ga watan Satumba.

Duk da cewa Amurka ce ta tsara tare da ingiza saka sabbin takunkumin, ta kuma matsa lamba aka amince da shi cikin gaggawa, shugaba Trump na ganin, matakin bai taka kara ya karya ba.

Hakan ya sa ya yi ta nanata cewa batun daukan matakin soji na nan a cikin zabin da zai iya amfani da su, kuma ko a ranar Juma’ar da ta gabata ma, Jakadar Amurka a Majalisar da mai ba Trump shawara kan harkar tsaro, sai da suka jaddada wannan matsayar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG