Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Yi Kashedi Kan Harajin Da Amurka Za Ta Sa Kan Shiga Da Karafuna


Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban China Xi Jinping

Kasar China tayi kashedi a kan babban tasiri da shirin harajin Amurka zai yiwa kasuwancin duniya, idan shugaban Amurka Donald Trump ya ci gaba da dora harajin kashi 25 cikin dari a kan karafan da ake shigo dasu daga kasashen waje.

Shugaban ma’aikatar harkokin kasuwanci da hukumar bincike na kasar China, Wang Hejun, ya fada a cikin wata sanarwa da yammacin Juma’a, cewa wannan harajin zai yi babban lahani ga huldan cinikayya da cibiyar kasuwanci ta duniya take kullawa kazalika zai yi mummunra tasiri a kan huldan cinikayya tsakanin kasashe.

Jami’in na China ya kara da cewa, idan har wannan matakin da Amurka ke niyar dauka ya tabbata, zai addabi muradun China kuma China zata yi aiki da kasashen da wannan lamari ya shafa don kare yancinta da muradunta.

A hali da ake ciki kuma Firayi Ministan Canada Justin Trudeau yace Canada ba zata amince da harajin da Trump ke niyar bullowa da shi a kan karafen da ake shigo dasu Amurka ba kuma yace a shirye yake ya kare masana’ntun kasarsa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG